in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin EXPO na Shanghai ya nuna cewa ingantuwar birni ita ce ta rayuwa
2010-04-30 17:42:38 cri

A ran 30 ga watan Afrilu da dare, a bakin kogin Huangpu da ya ratsa birnin Shanghai na kasar Sin, tare da wasan wuta da za a yi, za a kaddamar da bikin baje koli na kasa da kasa na EXPO na shekarar 2010 a birnin Shanghai. A cikin watanni 6 masu zuwa, kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa da yawansu ya kai 246 za su nuna wa jama'a wani gagarumin bikin baje koli na kimiyya da fasaha da kuma na al'adu, kuma za a bayyana ma'anar babban taken wannan biki, wato "birni mai kayatarwa da rayuwa mai inganci". A cikin farfajiyar bikin EXPO na Shanghai da fadinsa ya kai murabba'in kilomita 5.28, ba ma kawai za a ga ci gaban zamani da aka samu a duniya ba, har ma za a ga bambancin da ke kasancewa a tsakanin al'adu daban daban.

A cikin shekaru fiye da 100 da suka gabata, an shirya bukukuwan EXPO daga kasashen Turai zuwa nahiyar Amurka ta arewa, har ya zuwa nahiyar Asiya. Amma babbar ma'anar da ta kan kasance a yayin bukukuwan EXPO shi ne "kirkirowa". A yayin bikin EXPO na shekarar 1878 da aka yi a birnin Paris na kasar Faransa, an soma sanin wayar tarho da Bell, Alexander Graham ya kirkiro da na'urar daukar murya da Thomas Edison ya kirkiro. Haka kuma, a yayin bikin EXPO na shekarar 1939 da aka yi a birnin New York, an nuna akwatin talibijin da na'urar Robot, sannan a yayin bikin EXPO na shekarar 2005 da aka yi a birnin Aichi na kasar Japan, an nuna jirgin kasa mai tafiya da karfin manganadisu cikin sauri da ababen hawa maras gurbata muhalli.

1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China