Babban taken birnin Dusseldorf a yayin wannan bikin baje koli na Shanghai shi ne "Samun bunkasuwar tattalin arziki da rayuwa baki daya----Ana rayuwa da samun ci gaba mai dorewa a Dusseldorf".
Mataimakin magajin garin birnin Wilfried Kruse dake kula da harkokin sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da fasahohin sadarwa ya bayyana cewa, ana iya hada bunkasuwar tattalin arziki da tsara fasalin birni mai dorewa da kyautata ingancin rayuwar jama'a baki daya. Ya ce,
"Wannan ne hanyar da birnin Dusseldorf yake bi wajen samun bunkasuwa, kuma ya dace da babban taken bikin baje koli na Shanghai, wato Better City, Better Life. A wannan karo, za mu gwada wata hanyar da aka sake kafawa daga gabar kogin Rhine zuwa karkashin kasa. Hakan ya yi sanadiyyar komawar mazauna a yankin kogin Rhine. Bayan haka, wannan ra'ayi ta ma ya dace da tasharmu ta Medienhafen. Bayan da aka yi kwaskwarima, tsohuwar tashar jiragen ruwa ta kasance wata tashar zamani. A sakamakon haka, a ganina, wasu biranen kasar Sin za su iya samun darasi wajen sumun bunkasuwa."