in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da shugaban majalisar dokokin kasar Algeria da shugaban taron M.D.D a karo na 64
2010-04-30 16:12:26 cri

A ranar 30 ga wata, a birnin Shanghai, mataimakin shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugaban taron M.D.D a karo na 64 Ali Abdel Salam Triki da shugaban majalisar dokokin kasar Algeria Abdelkader Bensalah da suka zo kasar Sin domin halartar bikin bude taron baje-koli na Shanghai, inda ya yi lale marhabin da zuwansu, domin ganewa idonsu wannan gagarumin biki mai kayatarwa da ba za a manta da shi ba har abada.

Yayin da yake ganawa da Triki, Xi Jinping ya bayyana cewa, bikin baje-koli na duniya da kungiyoyin M.D.D na da ra'ayi kusan irin daya wajen sa kaimi ga mu'amala tsakanin kasashen duniya domin cimma burin samun bunkasuwa. Kasar Sin a matsayinta na wata kasa mafi girma tasowa kuma kasa mai kujerar din-din-din a cikin kwamitin sulhu na M.D.D, kasar Sin na tsayawa kan kiyaye tsarin mulki na M.D.D da sauke nauyin da ke bisa kanta, kuma kasar Sin ta yi hadin gwiwa mai ma'ana da M.D.D kan manyan batutuwan duniya da na shiyya-shiyya, kuma hakan ya ba da sakamako mai kyau.

Triki ya bayyana cewa, M.D.D ta dora muhimmanci sosai tare da yaba wa muhimmiyar rawar da kasar Sin da sauran kasashe masu tasowa ke takawa wajen nuna goyon baya ga aikin M.D.D, kuma M.D.D na fatan inganta hadin gwiwa da kasar Sin, domin kara ba da gudummawa ga aikin shimfida zaman lafiya da lumana a duniya.

Yayin da Xi Jinping ke ganawa da Bensalah, ya bayyana cewa, bikin baje-koli na duniya da aka shirya a wannan gami, shi ne biki karo na farko da za a yi a kasa mai tasowa, ba za a iya rasa goyon baya daga kasashe masu tasowa ba ciki har da kasar Algeria. Ya ce, kasar Sin na fatan yin kokari tare da kasar Algeria, domin kara inganta mu'amala da hadin gwiwa a dukkan matsayi a cikin majalisun dokokin kasashe biyu, domin ingiza dangantakar kasashen biyu daga dukkan fannoni.

Bensalah ya bayyana cewa, yana yin farin ciki da samun damar zuwa nan kasar Sin, domin halartar bikin baje-koli na Shanghai, watau wani gagarumin biki da ke shafar tattalin arziki da al'adu na kasashen duniya. Ya ce, kasar Sin kyakkyawar kawa ce ta kasar Algeria, kuma daya daga cikin manyan kasashen da suka amince da kafuwar kasar Algeria tun farko, kuma kasar Sin ta ba da taimako mafi girma ga kasar Algeria, kuma jama'ar kasar Algeria ba za su manta da wannan ba. Kasar Algeria tana fatan yin kokari tare da kasar Sin, domin kara ingiza dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare da ke tsakanin kasashen biyu da ta kara bunkasa har zuwa wani sabon matsayi (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China