in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hu Jintao ya gana da takwarorinsa na kasashen Kongo(Brazzaville) da Gabon
2010-04-29 20:41:42 cri

Ranar 29 ga wata, a birnin Shanghai, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da takwaransa na kasar Kongo(Brazzaville) Denis Sassou Nguesso, gami da shugaban kasar Gabon Ali Bongo, wadanda za su halarci wajen kaddamar da bikin baje-koli na kasa da kasa a birnin Shanghai.

Hu Jintao ya yi lale marhabin da halartar shugabannin kasashen biyu a wajen bude bikin EXPO na Shanghai, inda ya ce, bikin EXPO na Shanghai, wani muhimmin bikin kasa da kasa ne da kasar Sin zata shirya bayan gasar wasannin Olympics ta Beijing. Ya yi imanin cewa, sakamakon dimbin taimakon da kasashen dake tasowa suka bayar, ko shakka babu kasar Sin zata shirya wani kasaitaccen bikin baje-koli tare da cikakkiyar nasara. A nasu bangaren, Denis Sassou Nguesso, da Ali Bongo sun taya kasar Sin murnar gudanar da wannan gagarumin bikin dake jawo hankalin duniya baki daya.

Yayin da yake ganawa da takwaransa na kasar Kongo(Brazzaville) Denis Sassou Nguesso, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya ce, kasar Sin na mayar da hankali sosai kan karfafa huldar dake tsakanin kasashen biyu, haka kuma kasar Sin tana fatan yin kokari tare da kasar Kongo(Brazzaville), wajen karfafa hadin-gwiwarsu.

Sassou ya ce, kasarsa na fatan yin kokari tare da kasar Sin wajen inganta hadin-gwiwar kasashen biyu a fannin gina muhimman ayyukan biyan bukatun jama'a, ta yadda za'a himmatu ga bunkasuwar dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.

Har wa yau, yayin da yake yin shawarwari tare da takwaransa na kasar Gabon, Hu Jintao ya nuna cewa, kasar Sin tana fatan yin kokari tare da kasar Gabon, wajen fadada hadin-gwiwa a tsakaninsu.

A nasa bangaren kuma, Ali Bongo ya ce, bisa tushen girmama juna, da rashin yin katsalandan cikin harkokin gida na juna, dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa tsakanin kasashen Gabon da Sin tana bunkasuwa yadda ya kamata, haka kuma Gabon tana gamsuwa sosai a game da ci gaban huldar kasashen biyu.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China