in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manema labaru na kasa da kasa sun nuna yabo ga ayyukan shirya bikin baje koli na duniya na Shanghai
2010-04-29 18:04:23 cri

Ran 30 ga wata da dare, za a bude bikin baje koli na duniya wato EXPO a gefen kogin Huangpu a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin. Bikin EXPO na wannan karo ya jawo manema labaru kusan dubu 14 na sassan duniya daban daban, ciki har da dubban manema labaru daga ketare. Wadannan manema labaru sun nuna yabo ga ayyukan shirya bikin EXPO na Shanghai, kuma sun gamsu da wurin kwana da aikin hidima da aka gabatar ga manema labaru, akwai kuma masu ra'ayin cewa, bikin EXPO na Shanghai zai kara sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin kasa da kasa. Yanzu ga bayani filla filla

Babban take na bikin EXPO na Shanghai shi ne "birni mai kayatarwa, da rayuwa mai inganci", wannan shi ne karo na farko da za a yi bikin EXPO a wata kasa mai tasowa, yanzu akwai kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 264 da za su yi nune-nune a bikin EXPO, an kiyasta cewa akwai mutane fiye da miliyan 70 da za su ziyara bikin, wani dan jarida Philip Hoff daga kasar Switzerland ya ce, "Wannan wani karo ne na bikin EXPO mai kyau kwarai da gaske, kamar yadda kuka sani, a duk sassan kasar Switzerland, mazauna ba su wuce miliyan 7 ba, amma a cikin watanni 6 masu zuwa, bikin EXPO na Shanghai zai jawo mutane fiye da miliyan 70, wanda ninki ne sau 10 na yawan mutanen kasar Switzerland, wannan wani abu ne mai ban ta'ajibi."

1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China