in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu shirya baje koli na kasashe daban daban na jiran budewar farfajiyar bikin EXPO
2010-04-28 20:07:20 cri

Yau 28 ga wata ya rage mana kwanaki 3 a bude bikin baje kolin duniya wato EXPO a birnin Shanghai, inda kasashe daban daban da kungiyoyin kasashen duniya suke shirya suna jiran budewar farfajiyar bikin EXPO a hukunce a ranar 1 ga watan Mayu. An ce, yawan kasashe masu halartar bikin da fadin rumfunan da aka gina wa bikin da ba a taba samun irinsu a tarihi ba.

Hong Hao, shugaban hukuma mai kula da aikin bikin EXPO ta birnin Shanghai, ya yi bayani a yau cewa, zuwa yanzu, yawan bangagorin da suka halarci bikin EXPO na Shanghai ya kai 246, wadanda suka hada da kasashe 189, da kuma kungiyoyi 57.

An ce, an riga an gama aikin gina wasu rumfuna da kuma kawo karshen aikin tsara kayayyaki a ciki, rumfunan da suka kunshi rumfar kasashen Afirka, da ta kasar Jamus, da Australiya, da kungiyar agaji ta Red Cross da Red Crescent, da dai sauransu. Sai dai ana ci gaba da kokarin tsara kayayyakin baje koli a cikin wasu rumfuna. Sa'an nan masu fasaha na kasashen Turkiya, da Rasha, da Koriya ta Kudu, da Japan, da dai sauransu sun riga sun iso birnin Shanghai, inda suka fara gwajin nune-nunen fasaha da za su yi bayan da aka bude farfajiyar bikin EXPO, ta yadda za a kayatar da jama'ar da za su yi kallo a wajen. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China