Wang Xiaoqin ya kara da cewa, an fara samar da jinya kyauta tun ranar 15 ga watan Afrilu har zuwa ranar 15 ga watan Mayu mai zuwa. Sai dai game da wadanda ba su warke sosai ba bayan wata daya, za a ci gaba da kula da su har su warke sarai, kuma ba tare da karba musu kudi ba.
Alkaluman da aka rawaito mana sun shaida cewa, zuwa ranar 24 ga watan Afrilu, girgizar kasa da ta auku a gundumar Yushu ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 2203, da bacewar wasu 73, sa'an nan an samu mutane fiye da dubu 10 da suka samu raunuka a wajen bala'in. (Bello Wang)