in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An dasa aya ga kokarin da ake yi na neman tsira da rayuka a gundumar Yushu da girgizar kasa ta shafa
2010-04-24 20:17:50 cri
A yanzu haka dai, ana dab da kawo karshen kokarin da ake yi na neman tsira da rayuka a gundumar Yushu ta kasar Sin da girgizar kasa ta galabaita, kuma sojoji da 'yan sanda sun shiga wani mataki na gaba na farfado da zaman rayuwar al'umma.

Manjo janar Li Jun ya fadi haka ne a ranar 24 ga wata, kuma ya kara da cewa, bayan da aka bi kauyuka da kauyuka kuma gida zuwa gida a wani kokari na tsira da rayukan jama'ar da girgizar kasa ta rutsa da su, sojoji da 'yan sanda sun riga sun kammala duba ko ina. A mataki na gaba, sojoji za su karkata hankali zuwa kula da farfado da zaman rayuwar al'umma da samar da jiyya da rigakafin cututtuka da kafa tantuna ga makarantu da kuma ba da kariya ga al'adun kabilar Tibet. An ce, ya zuwa ranar 24 ga wata, gwamnatin kasar Sin ta tura sojoji da 'yan sanda sama da dubu 12 zuwa yankin da girgizar kasa ta shafa, wadanda suka tsira da rayukan jama'a 1584 tare da samar da jiyya ga wasu 18129.

Har wa yau kuma, kwanan baya, wasu karin shugabannin kasashen ketare da na kungiyoyin duniya sun aike da sakwanni zuwa ga shugabannin kasar Sin, don jajantawa gwamnatin kasar da jama'arta kan wannan girgizar kasa, ciki har da shugaban kasar Ghana, John Evans Atta Mills, da shugaban kasar Saliyo, Ernest Bai Koroma. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China