in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinawa mazauna kasashen waje sun ba da kyautar kudi ga gundumar Yushu da girgizar kasa ta shafa
2010-04-24 16:23:31 cri
Bala'in girgizar kasa da ya abku a gundumar Yushu ta lardin Qinghai na kasar Sin ya jawo hankalin dimbin Sinawa mazauna kasashen waje sosai, wadanda suka ba da kyauta kudi cikin himma da kwazo, abin da ya nuna dankon soyayya da ke tsakanin al'ummar Sin.

Ran 23 ga wata, kungiyar harkokin kasuwanci ta kasar Sin a kasar Bangladesh ta shirya taron ba da kyautar kudi a birnin Dhaka, inda Sinawa mazauna wurin da wakilan kamfanonin jari na kasar Sin fiye da 50 da ke kasar suka ba da kyautar kudi domin ba da gudummawa ga wuraren da ke fama da bala'in a gundumar Yushu. A karshen wannan gidauniya, yawan kyautar kudi da aka samu a wannan rana ya wuce dalar Amurka dubu 20.

Sa'an nan a ran nan, ofishin jakadancin kasar Sin a kasar Myanmar ya karbi kyautar kudi da yawanta ya wuce dalar Amurka dubu 50 daga hannun Sinawa mazauna wurin.

Haka zalika kuma, Sinawan da ke zaune a kasashen Pakistan da Faransa da dai sauransu su ma sun ba da kyautar kudi.

An labarta cewa, ya zuwa ran 23 ga wata da karfe 5 na yamma, bala'in girgizar kasa da ya abku a gundumar Yushu ta lardin Qinghai da ke arewa maso yammacin kasar Sin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 2192, yayin da wasu 78 suka bace.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China