in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta tsara ka'idoji kan tsugunar da wadanda girgizar kasa ta shafa a Yushu
2010-04-23 21:26:18 cri

Ran 23 ga wata, ma'aikatun kula da harkokin jama'a da kula da harkokin gidaje gami da kasuwanci ta kasar sun ba da shawarwari kan tsugunar da mazauna gundumar Yushu ta lardin Qinghai da ke fama da bala'in girgizar kasa a gajeren lokaci. Bisa shawararinsu, dole ne a bai wa ko wane iyali wani tanti ko kuma wani gidan wucin gadi da nufin samar musu wuraren kwana.

Sa'an nan kuma, wajibi ne a tsugunar da su a wuraren da ba za a iya samun yiwuwar aukuwar girgizar kasa da zabtarewar kasa daga tsaunuka da dai sauransu ba. Haka kuma, wajibi ne a yi kokarin magance gurbatar muhalli. Bayan haka kuma, tilas ne a samar musu da isasshen abinci da kayayyakin masarufi. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China