Shugaban kasar Kenya Mwai Kibaki ya nuna tausayawa da jajantawa jama'ar kasar Sin, kuma ya bayyana cewa, jama'ar kasar Kenya da ta kasar Sin za su hada kai tare.
Haka kuma shugabanni na kasashen Namibiya, Togo, Tunisiya, Afrika ta tsakiya, Morocco, Burundi da Djibouti sun nuna jaje ga jama'ar kasar Sin, kuma sun nuna imanin cewa, gwamnatin Sin da jama'arta za su iya cimma nasara wajen saukaka radadin bala'i daga indallahi.
Kana ofishin sakatariya na kungiyar raya kudancin kasashen Afrika wato SADC ya nuna jaje ga gwamnatin Sin da jama'arta da dangogin wadanda suka mutu.
Dadin dadawa kuma, kwanan baya, kasashen Belgium da Romaniya su ma sun mika jaje ga kasar Sin.(Bako)