Jaridar Leadership ta ce, jami'an 'yan sanda da wasu jama'a sun bayyana cewa, akalla mutum 10 sun bakunci lahira a sakamakon tsagewar kasa da ta afku a Somaliya.
Wannan ya faru ne a babban birnin kasar, wanda wasu daga cikin sojojin gwamnatinsu na daga cikin mamatan.
Wani wanda ya shaida faruwar hakan Abdulfatah ya ce, abin da ya auku ne cikin dare a kusa da ofishin 'yan sanda ke Magadishu, ya kara da cewa, mutum 10 sun mutu nan take ba tare da bata lokaci ba. Algyab wani jami'in 'yan sanda ya ce, 'yan uwansa ma'aikata mutum biyar sun mutu a lokacin da wannan abu ya auku.
Fadum Hassan, wani ma'aikacin asibitin kasar ya ce, mutane 20 da suka samu rauni suna kwance a asibiti, amma wasu na cikin mummunan yanayi.
Jama'a masu karatu, bayan haka kuma bari mu sake duba wani labari da muka samu daga jaridar Aminiya ta kasar Nijeriya, wadda aka fita a wannan mako, inda aka bayyana cewa, kasar Sudan ta yi fatali da sukan Amurka ga zaben kasar.
Jaridar Aminiya ta ce, jam'iyyar shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ta yi tafali da sukan zaben kasar da Amurka ta yi na cewa an yi magudi a cikinsa.
Wani kusa a Jam'iyyar NCP ta shugaba Al-Bashir, mista Ibrahim Ghandoor ya shida wa manema labaru cewa,
'Daya daga cikin muhimman hanyoyin da ake bi don zabe ya cika dukkan ka'idojin da duniya ta yarda da su, shi ne a gudanar da zabe na gaskiya ba magudi ba coge, kuma mun cimma wannan ka'aida.'
Mutanen kasar Sudan sun jefa kuri'a a tsakanin 11 zuwa 15 ga Afrilun nan domin zaben shugaban kasa da wakilan majalisar dokoki da wakilan yankuna da ya gudana a karkashin jam'iyyu da dama a karon farko sama da shekaru 20 da suka gabata.
Amurka ta hannun cibiyar hulda da kasashen waje ta kasar ta ce, zaben bai gudana cikin gaskiya da adalci ba, bayan da 'yan kallo suka ce ya gaza cimma ka'idar duniya kan zabe. Kakakin cibiyar Philip Crowley ya fada a Washinton cewa,
'Wannan ba zabe ba ne na gaskiya da adalci. A gaskiya bai cimma ka'idojin kasa da kasa kan zabe ba. Kuma ina jin ya kamata mu lura cewa, zabe muhimmin mataki ne na aiwatar da shirin zaman lafiya da zai kawo karshen yakin basasar shekaru tsakanin Arewa da kudancin Sudan.'
Ya ce, Washinton za ta ci gaba da aiki da gwamnatin Arewaci da ta Kudancin Sudan, a kokarin da take na gusawa gaba wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya, da kuma samun nasarar kuri'ar jin ra'ayin jama'a game da ba Kudancin Sudan 'yancin kai da ake sa ran gudanarwa a Janarairun badi.
NCP ta yi maraba da wannan tayi, inda Ghandoor ya ce,
'Muna maraba da hada kai da Amurka don aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya.'
Manyan masu kalubalantar Bashir a zaben, Sadik al-Mahdi na jam'iyyar Umma da Yasser Arman na tsohuwar kungiyar 'yan tawaye ta SPLM ta kudancin Sudan, sun janye daga takarar dab da fara zaben. Wannan ya share wa al-Bashir hanyar samun nasara. Sai dai an koka kan rashin isar kayan zabe mazabu a kan lokaci da bacewar rajistarsu da kai akwatunan zabe mazabun da ba nasu ba.(Danladi)