in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata babbar Jami'ar M.D.D ta nuna babban yabo ga aikin saukaka radadin bala'in girgizar kasa da kasar Sin ta yi
2010-04-23 14:21:52 cri

A ran 22 ga wata, a birnin Bangkok, mataimakiyar sakataren M.D.D kuma sakatariyar kwamitin ESCAP Noeleen Hezyer ta bayyana cewa, bayan abkuwar bala'in girgizar kasa a gundumar Yushu, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai daban daban don saukaka radadin bala'in girgizar kasar ba tare da bata lokaci ba, wannan abin yabawa ne daga jama'ar kasar.

Yayin da Noeleen Hezyer take ganawa da zaunanen wakilin kwamitin ESCAP Diao Muingsheng, ta bayyana cewa, yankuna daban daban na kasar Sin sun ba da taimako ga Yushu sosai, ba a iya ganin haka a wasu kasashe .

Noeleen Hezyer ta kara da cewa, gwamnatin kasar Sin ta saukar da tutar kasar zuwa rabin sanda don yin zaman makokin wadanda suka rasu a sakamakon bala'in girgizar kasa da ya abku a Yushu, wannan ya nuna girmama rayukan jama'a, tare da samun bunkasuwar al'ummar kasa.Yayin ganawar da suka yi, Noeleen Hezyer da Diao Mingsheng sun yi musayar ra'ayoyi a fannonin yaki da bala'u da yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China