in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(Sabunta) Kasa da kasa na ci gaba da nuna jaje game da bala'in girgizar kasa da ya abku a gundumar Yushu ta lardin Qinghai a kasar Sin
2010-04-22 20:53:49 cri

A ranar 20 da ta 21 ga wata, an kara samun shugabannin wasu kasashe ko na kungiyoyin shiyyoyi da dama da suka aike da sakwanni ga shugabannin kasar Sin, domin nuna jaje ga gwamnatin Sin da jama'arta game da bala'in girgizar kasa da ya abku a gundumar Yushu ta lardin Qinghai a kasar Sin.

Shugaban kasar Habasha Girma Wolde Giorgis ya nuna bakin ciki game da mutuwa da jikkatar mutane da yawa a sakamakon girgizar kasa, kuma ya nuna babban juyayi da jajantawa jama'ar Sin da dangogin wadanda suka mutu, kuma ya nuna imanin cewa, jama'ar Sin za su iya saukaka radadin wannan bala'i a karkashin shugabancin gwamnatin kasar Sin.

Shugaban kasar Tanzania Jakaya Mrisho Kikwete ya yi juyayi game da rasu rayuka da aka yi, kuma ya nuna tausayawa ga iyalan wadanda suke fama da bala'in.

Shugaban kasar Tunisiya Zine El Abidine Ben Ali ya nuna jaje da juyayi ga jama'ar kasar Sin.

Haka kuma, firaministan kasar Cape Verde José Maria Pereira Neves da shugaban majalisar dokokin kasar Aristides Raimundo Lima sun nuna jaje ga rashin da aka yi, kuma ya jajantawa jama'ar Sin da dangogin wadanda suka mutu.

Firaministan kasar Lesotho Pakalitha Mosisili ya nuna jaje ga rasa rayuka da aka yi, kuma ya yi fatan wadanda suka jikkata za su samu waraka cikin hanzari.

Haka kuma, shugaban majalisar dokoki na kasar Guinea-Bissau Raimundo Pereira ya nuna jaje ga dangogin wadanda suka mutu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China