in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu rawa na Togo za su nuna wasanni masu kayatarwa a bikin baje koli na duniya da za a yi a Shanghai
2010-04-22 19:56:39 cri

A gabannin bude bikin baje koli na kasa da kasa a birnin Shanghai na kasar Sin, cibiyar kula da harkokin nune-nune ta kasar Togo ta furta kwanan baya cewa, Togo ta shirya halartar bikin baje koli na duniya da za a yi a birnin Shanghai. Haka kuma, an kammala gina rumfar nune-nune ta Togo a farfajiyar bikin.

An labarta cewa, a yayin bikin baje koli na kasa da kasa da za a yi a Shanghai, Togo za ta tura shahararriyar kungiyar masu rawa ta Ziguidi domin nuna wasanni na tsawon kwanaki 14 a Shanghai da wasu sassan kasar Sin. Shugaban kungiyar Ziguidi ya nuna cewa, tabbas ne kungiyarsa za ta nuna wa 'yan kallo daga sassa daban daban na duniya wasanni masu kayatarwa. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China