Madam Bokova ta bayyana wa 'yan jarida a wannan rana cewa, ta nuna alhini ga mutuwa da raunatar mutane masu yawa a sakamakon girgizar kasa da ta abku a yankin Yushu. Ta ce, bayan abkuwar girgizar kasar, tana sa lura sosai kan halin da ake ciki a yanki mai fama da bala'in. Ta gano da cewa, yanki mai fama da bala'in ya dala iyakar teku sosai kuma ana sanyi sosai a yankin, sabo da haka, ana fuskantar matsaloli masu yawa yayin da ake gudanar da aikin ceto. Amma gwamnatin kasar Sin ta yi kokarin ceton mutane masu fama da bala'in.
A ran 21 ga wata, an gudanar da aikin nuna alhini ga mutane da suka rasu a sakamakon girgizar kasa a dukkan kasar Sin. A wannan rana, Bokova ta sake nuna ta'aziyya ga mutane da suka mutu a yankin Yushu.
Madam Bokova ta taba mika wata wasika ga firaministan kasar Sin Wen Jiabao, inda ta ce, idan kasar Sin tana bukatar wani abu daga hukumar UNESCO, to za ta ba da gudummawa ga yanki mai fama da bala'in.(Zainab)