Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya bayar, an ce, Hui Liangyu ya bayyana a gun wani taro na sashen ba da umurni kan aikin ceto cewa, ya kamata a tabbatar da aikin karba da rarraba da yin amfani da kudin taimako da kayayyakin taimako bisa tsarin dokoki, da tabbatar da yin amfani da wadannan kayayyaki a yanki mai fama domin amfanawa girgizar kasa da mutane masu fama da bala'in, da bayyana yawan kayayyakin taimako da wuraren da suka isa ga jama'a, da yarda da bangarori daban daban da kafofin watsa labaru na gida da na waje su sa ido kan yanayin da ake ciki wajen gudanar da aikin, da kuma hada kai tare da hukumomin sa ido da na yin bincike wajen kara sa ido kan halin da ake yin amfani da kayayyakin taimako.
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya bayar, an ce, ya zuwa ranar 21 ga wata da karfe 5 na yamma, girgizar kasa da ta abku a yankin Yushu na lardin Qinghai na kasar Sin ta haddasa mutuwar mutane 2183, kuma mutane 12135 sun ji rauni, sannan kuma da bacewar mutane 84.(Zainab)