Shugabanni na kasashen Benin, Tanzania, kamaru, Burundi, Somaliya sun jajantawa jama'ar kasar Sin da dangogin wadanda suka mutu, kana sun yaba wa matakan da gwamnatin Sin ta dauka domin saukaka radadin bala'in girgizar kasa da ceton mutane.
Babban jami'in da ke kula da harkokin 'yan gudun hijira na M.D.D Antonio Guterres da sakatare janar na kawancen kasashen Larabawa Amar Mahmoud Moussa sun nuna jaje ga dangogin wadanda suka mutu, kuma sun yi fatan wadanda suka jikkata za su samu waraka cikin hanzari, kazalika sun nuna imani cewa, gwamnatin Sin da jama'arta za su iya wajen warware matsalar da bala'in girgizar kasa ya haifar.(Bako)