Sa'an nan ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin tana daukar matakai masu yakini domin samar da isasshen naman sa da na tunkiya a kasuwannin wuraren da bala'in ya rutsa da su a lardin Qinghai. Tana kuma tuntubar lardunan Sichuan, Shaanxi, Gansu da jihar Ningxia, da nufin shirya yin jigilar kayayyakin lambu zuwa wuraren da bala'in ya yi wa ta'adi. Haka zalika, a karkashin shugabancin ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin, masana'antun dafa abinci da ke Qinghai, Sichuan da kuma jihar Tibet sun je wuraren da bala'in ya shafa tare da danyun kayayyakin abinci, inda suke dafa wa masu fama da bala'in abinci. (Tasallah)