in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tsugunar da jama'a da ba su tallafin kayayyaki a Yushu
2010-04-21 16:58:39 cri

Bala'in girgizar kasa mai karfin maki 7.1 bisa ma'aunin Ritcher da ya abku a ranar 14 ga wannan wata a gundumar Yushu dake lardin Qinghai na kasar Sin, ya ritsa da mutane sama da dubu 100. Rahoto daga filin sukuwar dawaki dake garin Jiegu na gundumar Yushu, wanda ya kasance matsuguni mafi girma na jama'ar da bala'in ya shafa ya ce, an tsugunar da mutanen da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su, da ba su tallafin kayayyaki yadda ya kamata.

Filin sukuwar dawakin yana yammacin garin Jiegu ne. Bayan abkuwar girgizar kasar, wannan wuri ba ma kawai ya karbi mutane daga gundumar Yushu ba, har ma da wasu mutane daga sauran gundumomi makwabta. Yanzu, an riga an kafa tantuna dubu 10 a wannan filin sukuwar dawaki, kuma yawan mutanen da suke zaune a nan ya zarce dubu 10.

Wani jami'i daga sashin bada jagoranci a wurin ya gayawa wakilinmu cewa, a kowace rana, su kan samu abinci da tantuna da bangarori daban-daban suka bayar kyauta, sa'an nan za su baiwa mutanen da suke fama da bala'in girgizar kasa, inda ya ce: "A wannan matsuguni, mun rarraba kayayyakin tallafi ga mutane bisa garuruwa da suka fito ba tare da bata lokaci ba. Mun tura kayayyaki zuwa yankuna daban-daban, sa'an nan mun raba su ga kowane mutum dake wurin."

Gaba daya an tsugunar da mutane 3112 a wani matsuguni na garin Baizha na gundumar Xiangqian dake filin sukuwar dawaki. Shugaban garin, Dala Wangchen ya nuna cewa: "Bisa halin da ake ciki da yawan mutanen da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su, mun tabbatar da cewa, kowane mutum zai samu tallafin abinci, da tantuna, gami da tsabtaccen ruwan sha."

1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China