in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana zaman makoki a duk fadin kasar Sin
2010-04-21 11:31:24 cri

Domin nuna babban alhini ga mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon bala'in girgizar kasa da ta abku a gundumar Yushu dake lardin Qinghai na kasar Sin, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta yanke shawarar cewa, a yi zaman makoki a ranar 21 ga watan Afrilu na shekara ta 2010, inda aka sassauto da tutocin kasar a dukkan kasar Sin da ofisoshin jakadancin kasar dake kasashen ketare, gami da dakatar da dukkanin shagulgula. Wannan ne karo na biyu da aka yi zaman makoki a duk fadin kasar Sin don nuna alhini ga mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon bala'in girgizar kasa tun bayan abkuwar bala'in girgizar kasa a shekarar 2008 a Wenchuan.

A ran 21 ga wata da sassafe, a filin Tian'anmen, an sassauto da tutar kasa. Kuma a ran nan da karfe 10 na safe, a birnin Beijing, jama'a ta kabilu daban daban, tare da Hu Jintao, Wu Bangguo, Wen Jiabao, Jia Qinglin da sauran shugabannin jam'iyyar kwaminis ta Sin da gwamnatin kasar Sin sun nuna alhini ga mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon bala'in girgizar kasa kuma sun yi shiru na tsawon mintoci 3.

A garin Jiegu na Yushu dake fama da bala'in, fararen hula na kabilu daban daban sama da dubu daya sun taru a filin gwamnatin garin don nuna alhini ga mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon bala'in. Kuma a kan hanyoyi da tituna na birnin Xining, an hura usur wa motoci. Mutane na kabilu daban daban sun shiga zaman makoki ta hanyoyi daban daban don nuna alhini ga mutanen da suka rasa rayukansu.

A ran nan kuma, an dakatar da dukkan shagulgula a bikin baje koli na duniya na Shanghai. Dakin baje koli na Qinghai ya shirya zaman makoki na musamman don nuna jejeto ga mutanen da suka rasa rayukansu.

Ban da haka kuma, dukkan hukumomin gwamnati na Hongkong da Macau sun sassauto da tutoci a yau.

Ofisoshin jakadun kasar Sin dake kasashen ketare sun yi zaman makoki don nuna alhini ga mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon bala'in, kuma Sinawa dake ketare da mutanen ketare sun halarci zaman don nuna jejeto ga mutanen da suka rasu.

Tun daga ranar 20 ga wata da karfe 12 na dare, babban gidan talabijin na kasar Sin wato CCTV ya fara watsa shirye-shirye na musamman don nuna alhini ga mutanen da suka rasu.

A ran 14 ga wata, an yi girgizar kasa mai karfin digiri 7.1 a gundumar Yushu ta lardin Qinghai. Ya zuwa ran 20 ga wata, yawan mutanen da suka mutu a sakamakon girgizar kasar ya kai 2039.(Asabe)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China