in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin kasar Sin tana gudanar da aikin kwantar da hankalin jama'ar ke fama da girgizar kasa yadda ya kamata
2010-04-21 10:00:28 cri

A gun taron manema labaru da aka saba shiryawa a ran 20 ga wata a nan Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Jian Yu ta bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana gudanar da aikin kwantar da hankalin jama'a ke fama da girgizar kasa yadda ya kamata.

Ta bayyana cewa, a halin yanzu, akwai isassun ma'aikatan samar da agaji, kuma ana yin safarar kayayyakin saukaka radadin bala'in zuwa wuraren da bala'in ya yi musu barna. Kuma an samar da jinya ga wadanda ke fama da bala'in jiyya, a sa'i daya kuma, gwamnatin kasar tana girmama addinai da kuma al'adun gargajiya da mazauna wurin suke bi, tana kuma gudanar da aikin kwantar da hankalinsu a kai a kai. Bayan haka kuma, bangaren kula da harkokin addinai na kasar ya kaddamar da shirin yin addu'a da yin ban kwana ga wadanda suka rasu a sakamakon bala'in.

Jiang Yu ta kara da cewa, a halin yanzu, gwamnati da jama'ar kasar Sin suna yin kokari wajen gudanar da ayyukan saukaka radadin bala'in. Sinawa mazauna kasashen waje da 'yan kabilar Tibet sun mai da hankali sosai kan wuraren da bala'in ya yi wa ta'adi, kuma sun nuna jejeto ta hanyoyi daban daban.

Ban da haka kuma, Jiang Yu ta bayyana cewa, ya zuwa ran 20 ga wata, kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da na shiyyoyi fiye da 150 sun mika wa gwamnatin da jama'ar kasar sakwannin jaje. Kuma gwamnatin da jama'ar kasar Sin su na godiya a gare su kwarai da gaske.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China