in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumomin kasar Sin dake ketare suna zaman makoki domin bala'in girgizar kasa a Yushu
2010-04-21 09:53:15 cri

Domin nuna babban alhini ga mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon bala'in girgizar kasa da ya abku a gundumar Yushu dake lardin Qinghai na kasar Sin, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta yanke shawarar cewa, za'a yi zaman makoki a ranar 21 ga watan Afrilu na shekara ta 2010. Ofisoshin jakadanci dake ketare da hukumomin kasar Sin dake ketare da kuma Sinawa dake zama a ketare suna zaman makoki a wannan rana. A kwanakin baya, kafofin yada labaru na kasashen ketare sun darajanta aikin ceto da sojojin kasar Sin ke yi a Yushu.

A ran 21 ga wata da sassafe, karkashin jagorancin Li Huishuai, jakadan Sin dake kasar Rasha, jami'an ofishin jakada sama da dari daya suna zaman makoki don nuna jejeto ga mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon abkuwar bala'in. Kuma ofishin jakadan kasa Sin dake Sidney ya sassauto da tutar kasar Sin don nuna alhini ga mutanen da suka rasu a sanadiyyar bala'in.

Ofishin jakadan kasar Sin dake kasar Faransa ya jagoranci Sinawa dake zama a Faransa da daliban dake yin karatun a kasar kallon bikin tattara tallafin kudi don taimakawa Yushu da gidan talabiji na tsakiyar kasar Sin wato CCTV ya yi a ran 20 ga wata da dare, kuma sun ba da tallafin kudi don taimakawa mutanen dake fama da bala'in.

A kwanakin baya, kafofin yada labaru na kasashen ketare sun darajanta aikin ceto da sojojin kasar Sin ke yi a Yushu, kuma suna ganin cewa, an horas da sojojin kasar Sin da kyau, kuma sun gudanar da aikin ceto cikin gaggawa.

A ran 14 ga wata da ran 15 ga wata, kamfanin dillancin labaru na Faransa wato AFP ya ba da labaru a jere game da gwamnatin kasar Sin ta tura tawagogin aikin ceto zuwa yankin cikin dan gajeren lokaci. A ran 14 ga wata, tashar Internet ta jaridar 'Lianhe Zaobao' ta kasar Singapore ta ba da labari cewa, bayan da bala'in girgizar kasa ya abku, rundunar soja ta lardin Qinghai da ta Lanzhou da kuma rundunar jiragen saman soja sun tura sojoji da kayayyakin tallafi zuwa yankin cikin gaggawa don gudanar da aikin ceto. A ran 15 ga wata, kamfanin dillancin labaru na kasar Amurka wato AP ya ba da labari cewa, ko da yake halin yin aikin ceto ba shi da kyau, amma sojojin kasar Sin su kan tinkari bala'i da kyau.

Ban da haka kuma, kafofin yada labaru da yawa sun gabatar da cewa, rundunar soja ta kasr Sin ta gudanar da aikin ceto cikin mummunar yanayi. Jaridar Daily Telegraph ta ba da labari cewa, masu aikin ceto suna fama da matsalolin lalacewar hanyoyi da kuma iska mai karfi dake bugawa da rashin iskan numfashi a babban tudu, amma duk da haka, sojojin yantar da jama'ar kasar Sin suna yin iyakacin kokari tare da masu aikin ceto don ceton mutanen dake fama da bala'in.(Asabe)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China