in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tara Yuan biliyan 2.175 a wajen taron bayar da kudi na musamman ga yankin Yushu
2010-04-21 09:25:06 cri

A ran 20 ga wata da dare, an gudanar da taro na musamman na bayar da kudin taimako ga yankin Yushu a gidan babban telebijin na kasar Sin wato CCTV, kana an watsa bikin kai tsaye ta talabijin na CCTV. An gudanar da bikin har na tsawon sa'o'i 3 da rabi, inda aka tattara kudin taimako Yuan biliyan 2.175.

Ma'aikatar kula da harkokin farfaganda na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da hukumar kula da harkokin radio da telebijin ta kasar da kuma ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar sun wallafa wannan taro, inda aka bayar da wasu labarai game da aikin ceto da aka gudanar a mako daya bayan abkuwar girgizar kasa a yankin Yushu, da yin wasanni da aikin bayar da kudin taimako don jajantawa jama'a masu fama da bala'in a madadin dukkan jama'ar kasar Sin. Ban da wannan, an bayar da kudin taimako kai tsaye a gun taron, kana masu kallon taron ta kwatunan telebijin sun bayar da kudin taimako ta hanyar buga waya.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China