Gwamnatin kasar Sin ta yanke shawarar gudanar da ayyukan nuna ta'aziyya, haka kuma dukkan yankunan kasar Sin da ofisoshin jakadancin kasar Sin da ke a kasashen waje za su saukar da tuta zuwa rabin sanda don yin ta'aziyya, kuma an dakatar da ayyukan nishadi, don nuna ta'aziyya ga rasuwar mutane a sakamakon bala'in girgizar kasa da ta abku a Yushu.(Abubakar)