in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasa da kasa na ci gaba da jajanta wa kasar Sin kan girgizar kasar da ta galabaitar da ita
2010-04-20 21:32:19 cri
Daga ranar 19 zuwa 20 ga wata, karin wasu shugabannin kasashen waje da jami'an kungiyoyin duniya da na shiyyoyi sun buga waya ko aika wasiku zuwa shugabannin kasar Sin, domin nuna jaje ga gwamnatin kasar Sin da jama'arta kan girgizar kasar da ta afka wa gundumar Yushu ta lardin Qinghai na kasar, ciki har da shugaban kasar Aljeriya, Abdelaziz Bouteflika da shugaban kasar Cote d'Ivoire, Laurent Gbagbo, da shugaban kasar Senegal, Abdoulaye Wade, wadanda suka nuna jaje ga jama'ar kasar Sin da iyalan wadanda suka riga mu gidan gaskiya, tare kuma da nuna goyon baya ga harkokin agaji da Sin ke gudanarwa.

Har wa yau kuma, babbar kwamishiniyar hukumar kula da hakkin bil Adam ta MDD, Madam Navanethen Pillay ta bayyana bakin cikinta kan asarar rayuka da aka yi, tare da nuna ta'aziyya ga iyalan wadanda suka mutu. Ta kuma yi imanin da cewa, bisa jagorancin gwamnatin kasar, Sin za ta haye wahalhalun da take fama da su.

Sai kuma shugaban kwamitin tarayyar Afirka, Jean Ping wanda ya nuna alhini ga iyalan wadanda suka mutu, ya kuma yaba wa gwamnatin kasar Sin kan yadda ta samar da agaji cikin hanzari nan da nan bayan aukuwar girgizar kasar.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China