in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare janar na kawancen kasashen Larabawa ya nuna jaje ga kasar Sin game da abkuwar girgizar kasa a gundumar Yushu ta lardin Qinghai a kasar
2010-04-20 21:19:05 cri
A ranar 19 ga wata, sakatare janar na kawacen kasashen Larabawa Amr Moussa ya aika da sako ga ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi domin nuna jaje game da abkuwar bala'in girgizar kasa a gundumar Yushu ta kasar Sin.

A cikin sakon, Moussa ya yi ta'aziyya ga mutanen da suka rasu a sakamakon girgizar kasa da aka yi a gundumar Yushu ta lardin Qinghai a kasar Sin, kuma ya yi fatan wadanda suka jikkata za su samu waraka cikin hanzari, haka kuma, ya yi imani cewa gwamnatin Sin da jama'arta za su iya haye wahalhalun da ke gabansu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China