Firaministan kasar Tanzania Mizengo Kayanza Peter Pinda ya jajantawa gwamnatin kasar Sin da jama'arta bayan abkuwar girgizar kasar, kana yana nuna yabo ga kasar Sin da ta dauki matakan ceto ba tare da bata lokaci ba. Ya kuma nuna yabo ga shugaban kasar Sin Hu Jintao da firaminstan kasar Wen Jiabao da suka isa yanki mai fama da bala'in, da ba da jagoranci ga aikin ceto, da zama tare da jama'a masu fama da bala'in a lokacin.
Ministan harkokin waje na kasar New Zealand Murray McCully ya bayar da wata sanarwa, inda ya ce, kasar Sin tana da wani tsari mai inganci na tinkarar bala'u cikin gaggawa. A matsayin wata muhimmiyar abokiyar kasar Sin, kasarsa za ta ba da taimakon kudi da ya kai kimanin dala dubu 280 ga yankin Yushu.
Jaridar Wall Street Journal ta kasar Amurka ta bayar da wani labari, inda ta ce, an fara yin jigilar kayayyakin taimako zuwa yankin Yushu. Kazalika shugaba Hu Jintao ya kammala ziyararsa da wuri a nahiyar Latin Amurka, kuma ya isa yankin Yushu a ran 18 ga wata don ba da jagoranci ga aikin ceto. Shugabannin kasar Sin sun taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da aikin ceto. Jama'ar dake zauna a yankin sun bayyana cewa, ziyarar da Hu Jintao da Wen Jiabao suka kai a yankin, tasa mutane sun kwantar da hankali.(Zainab)