in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a ci gaba da kokarin yaki da bala'in girgizar kasa
2010-04-20 10:13:33 cri

Ranar 19 ga wata, a nan birnin Beijing, mataimakin firaministan kasar Sin, kuma babban mai bada umurni na sashin bada jagoranci ga ayyukan yaki da bala'in girgizar kasa na majalisar gudanarwa ta kasa, Hui Liangyu ya jaddada cewa, kamata ya yi a ci gaba da kara kokari wajen yaki da bala'in girgizar kasa yadda ya kamata, da gudanar da bincike gami da tsara shirin sake farfadowa bayan abkuwar bala'in ba tare da bata lokaci ba.

A yayin wani taron da sashin bada jagoranci ga ayyukan yaki da bala'in girgizar kasa ya shirya a wannan rana, Hui Liangyu ya ce, ya kamata a ci gaba da gudanar da ayyukan yaki da bala'in girgizar kasa yadda ya kamata, ciki har da zakulo mutanen da bala'in ya ritsa da su, da yiwa mutanen da suka ji rauni jinya, da sake tsugunar da jama'a da suke fama da bala'in, da sake farfado da muhimman ababen biyan bukatun jama'a, gami da yin rigakafin barkewar cututtuka masu yaduwa, ta yadda jama'a za su samu abinci, da ruwan sha mai tsabta, da isassun tufafi da bargunan sanyi, tare kuma da tantuna da sauransu.

Mista Hui ya kara da cewa, ya zama dole a tsara shiri da jadawalin sake farfadowa bayan abkuwar wannan bala'i ba tare da bata lokaci ba, da kuma aiwatar da shi cikin sauri.

Har wa yau, rahoto daga kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya ce, zuwa karfe 10 na yammacin ranar 19 ga wata, adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon mummunan bala'in girgizar kasa da ya abku a gundumar Yushu dake lardin Qinghai na kasar Sin ya kai 2039, tare da bacewar mutane 195, kuma yawan mutanen da suka ji raunuka ya kai 12135, ciki har da 1434 wadanda suka ji rauni mai tsanani.

Bugu da kari kuma, zuwa karfe 6 na yammacin ranar 19 ga wata, gaba daya an samu wasu kananan girgizar kasa har sau 1227, ciki kuwa har da guda 12 wadanda karfinsu ya zarce maki 3 bisa ma'aunin Richter.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China