in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya sun ci gaba da jajantawa kasar Sin kan bala'in girgizar kasa a Yushu na lardin Qinghai
2010-04-20 09:42:38 cri

A ran 18 ga wata da kuma a ran 19 ga wata, wasu shugabannin kasashen ketare da na kungiyoyin kasashen duniya da na yankuna sun mika wasiku da buga waya ga Hu Jintao, shugaban kasar Sin da Wu Bangguo, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da firaministan kasar Sin Wen Jiabao don nuna jajantawa ga gwamnatin kasar Sin da jama'ar Sin kan bala'in girgizar kasa a Yushu na lardin Qinghai.

Sarauniyar kasar Ingila, Queen Elizabeth Ⅱ ta nuna jejeto ga mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon bala'in, kuma ta nuna jajantawa ga iyalan mutanen da suka mutu da mutanen da suke fama da bala'in.

Francois Fillon, firaministan kasar Faransa ya jajantawa jama'ar kasar Sin.

Rupiah Bwezani Banda, shugaban kasar Zambia ya nuna bakin ciki sosa ga hasarar da bala'in ya haddasa, kuma yana fatan za a samu nasarar aikin ceto.

Ismail Umar Guelleh, shugaban kasar Djibouti da Fouad Mebazaa, shugaban majalisar dokoki na kasar Tunisia sun nuna jejeto ga mutanen da suka mutu a sakamakon bala'in, kuma ya jajantawa iyalan mutanen da suka mutu da jama'ar Sin.

Amadou Toumani Toure, shugaban kasar Mali ya jajantawa jama'ar kasar Sin da iyalan mutanen da suka rasa rayukansu, kuma yana fatan mutanen da suka ji rauni za su samu sauki da sauri.

Helen Clark, shugaban hukumar UNDP ta M.D.D. ya nuna jejeto ga mutanen da suka mutu a sakamakon bala'in, da jajantawa iyalan mutanen da suka mutu da jama'ar Sin, kuma ya nuna babban yabo ga matakan ceto da gwamnatin Sin ta dauka bayan abkuwar bala'in, kana ya nuna imani ga karfin gwamnatin Sin wajen yaki da bala'in da gudanar da aikin ceto yadda ya kamata.

Hukumar UNHSP ta M.D.D. ta nuna jejeto ga mutanen da suka mutu sakamakon bala'in, kuma yana fatan mutanen da suka ji rauni za su samu sauki.

Ban da haka kuma, Sashen sakatariya na kungiyar kasashen Latin American da Caribbean ya jajantawa gwamnatin Sin da jama'ar kasar, da nuna goyon baya wajen farfado da yankin dake fama da bala'in.(Asabe)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China