in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta amsa tambayoyi game da gudummawar da kasashen duniya suke bayarwa domin yaki da girgizar kasa
2010-04-19 20:31:07 cri

A ranar 18 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Jiang Yu ta zanta da manema labaru game da gudummawar da kasashen duniya suke bayarwa domin aikin saukaka radadin girgizar kasa da ceton mutane.

Yayin da wani dan jarida ya yi tambayar cewa, bayan da girgizar kasa ta abku a gundumar Yushu ta lardin Qinghai a kasar Sin, mene ne matakai da kasar Sin za ta dauka game da aniyar ba da gudummawa da wasu kasashen duniya suka bayar domin ceton mutane? Jiang Yu ta ce, bayan da aka yi girgizar kasa a gundumar Yushu ta lardin Qinghai na kasar Sin, kasashen duniya sun nuna jejeto tare da dora muhimmanci sosai game da aikin saukaka radadin girgizar kasa da ceton mutane, kuma wasu kasashe da kungiyoyin duniya sun bayyana aniyar ba da gudummawa ga kasar Sin, wannan ya nuna dankon zumunci a tsakanin jama'ar kasar Sin da ta sauran kasashen duniya, game da hakan, gwamnatin Sin tana maraba tare da nuna sahihiyar zuciya gare su, kuma ta yi bayani kan kaddamar da asusun ajiya domin karbar kudin taimako. Yanzu, gwamnatin Sin na yin iyakacin kokari domin gudanar da aikin saukaka radadin girgizar kasa da ceton mutane, an yi ta tura ma'aikata masu aikin ceto da kayayyaki zuwa wuraren da ke fama da girgizar kasar. Haka kuma, An yi imani cewa, a sakamakon kokarin da jama'ar kasar Sin ke yi da goyon baya daga kasashen duniya, jama'ar da ke fama da girgizar kasar za su iya cimma nasara wajen daidaita batun girgizar kasa, da kuma sake gina kyawawan gidajensu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China