in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin yada labarai sun nuna yabo kan zuwan shugabannin Sin yankin da girgizar kasa ta rutsa da shi cikin hanzari
2010-04-19 20:22:44 cri

Da aukuwar girgizar kasa a gundumar Yushu da ke lardin Qinghai na kasar Sin, nan da nan shugabannin kasar Sin suka isa yankin, lamarin da ya sami yabo daga kafofin yada labarai.

A sabili da girgizar kasar, shugaban kasar Sin, Hu Jintao ya takaita wata ziyarar da yake yi a ketare, don kai ziyara zuwa gundumar Yushu da ke fama da bala'in. Ya ce, "a wannan lokaci mai wahala, ya kamata in kasance tare da jama'ata, in sa hannu cikin ayyukan samar da agaji." Jawabin nasa ya sosa ran jama'a, haka kuma jawo hankalin dimbin kafofin yada labarai.

Sharhin da jaridar Xinjingbao ta bayar ya yi nuni da cewa, shugaban kasar Sin ya kawo karshen ziyararsa a ketare kafin lokacin da aka tsai da, sabo da yadda ake samar da agaji da kuma wahalhalun da jama'a ke fama da su sun janyo hankalinsa sosai.

Har wa yau kuma, jaridar People's Daily ta yi sharhin cewa, da aukuwar girgizar kasa, nan da nan shugabannin Sin suka je yankin da ke fama da bala'in domin ba da jagoranci kan ayyukan samar da agaji, abin ya shimfida harsashi mai inganci ga samun nasarar samar da agaji.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China