A yayin wani taron da aka yi kan lamarin, Mr. Jia ya nuna cewa, ana fama da wahala sosai wajen samar da agaji a Yushu da bala'in ya rutsa da ita, dan haka dole ne hukumomi na matakai daban daban da abin ya shafa su je wuraren da bala'in ya abku, su jagoranci da kuma taimakawa mutane wajen ba da agaji da yin kokarin kubuta da kansu. Sa'an nan ofisoshin jakadancin kasar Sin a kasashen waje wajibi ne su saka bibbiyu su karbi 'yan kabilar Tibet mazauna kasashen waje, wadanda suka yi shirin dawowa kasar Sin don jajanta wa iyalansu da ba da kyautar kudi, su kuma ba su taimako.
Haka zalika, Mr. Jia ya jaddada cewa, a yayin da aka yi kokarin farfado da wuraren da bala'in ya shafa a lardin Qinghai, wajibi ne a sa muhimmanci kan wuraren da aka fi samun 'yan kabilar Tibet.(Tasallah)