Lokacin da aka samu rahoton aukuwar girgizar kasa mai karfin maki 7.1 bisa ma'aunin Richter a ranar 14 ga wata a gundumar Yushu ta lardin Qinghai, Shugaba Hu Jintao yana birnin Washington na kasar Amurka inda ya halarci shawarwarin da aka yi don neman hana yaduwar makaman nukiliya, daga bisani ya kai ziyara a kasar Brazil. Bayan haka kuma, shugaban ya koma kasar Sin a ranar 17 da yamma kafin lokacin da aka tsara. Nan da nan, Hu ya wuce gundumar Yushu a ranar 18 da safe, da kuma yin rangadi a kauyen Zhaxidatong inda aka tabka mummunar hasara sakamakon girgizar kasa. A gaban baraguzan gidaje, Hu ya rike hannun wani mazaunin wurin yana cewa, 'Za mu yi kokarin ceto wadanda suke karkashin baraguzan gidaje. Duk da cewa muna samun mutanen da ke da sauran numfashi a karkashin kasa, to, za mu yi bakin kokarin kubutar da su!'