An labarta cewa, daga cikin wadannan kudade yuan biliyan 20, za a kebe kudin Sin yuan miliyan dari 8 domin kyautata ingancin gidajen kwana da yawansu zai kai dubu dari 2 a yankunan karkara, sannan za a kebe kudin Sin yuan biliyan 12 da miliyan dari 6 domin kyautata gidajen kwana da yawansu zai kai dubu 63.7 a birane, har ma za ta kebe kudin Sin yuan biliyan 1 da miliyan dari 5 domin gina gidaje masu rahusa da yawansu zai kai murabba'in mita miliyan 1 a birane. Bugu da kari, za a kebe kudin Sin yuan biliyan 5 da miliyan dari 7 domin sake gina gidajen kwana ga wadanda suke zaune a yankunan da suka gamu da bala'in girgizar kasa mai tsanani sosai a shekarar 2008.