in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dole ne a bincike yadda ake amfani da kayayyakin jin kai da kudi da aka kebe wa yankin Yushu
2010-04-19 09:52:43 cri
A ran 18 ga wata, lokacin da yake rangadin aiki a yankin Yushu, inda ake fama da bala'in girgizar kasa, Mr. Liu Jiayi, shugaban hukumar kula da aikin binciken kudi ta kasar Sin ya jaddada cewa, hukumomin binciken kudi na matakai daban daban na kasar Sin za su yi namijin kokari wajen sa ido kan yadda ake rarraba kayayyakin jin kai da kuma yin amfani da kudade da aka kebe wa yankin. Mr. Liu ya ce, tabbas ne za a binciki wadanda suka canja akalar irin wadannan kudade da kayayyakin jin kai.

Mr. Liu Jiayi ya kara da cewa, hukumomin binciken kudi za su tabbatar da ganin an tattara da rarraba da kuma yin amfani da kayayyakin jin kai da kudade a fili cikin adalci ta hanyar aikin binciken kudi. Sannan za su sanar da sakamakon aikin binciken kudi da kuma gabatar da ra'ayoyin kyautata aiki ga gwamnatin wurin. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China