in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An ceci mutane dubu 11 da suka ji rauni a yayin girgizar kasa da ya abku a gundumar Yushu
2010-04-19 09:49:12 cri

Wakilinmu ya ruwaito mana labari daga hukumar kiwon lafiya ta lardin Qinghai cewa, ya zuwa ran 18 ga wata da karfe 4 na yamma, an ceci mutane dubu 11 da suka ji rauni a sakamakon girgizar kasa da ya abku a gundumar Yushu, yanzu, ana gudanar da ayyukan ba da jiyya da rigakafin annobar cuta yadda ya kamata.

Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya bayar, an ce, yawan mutanen da aka ceto daga bala'in girgizar kasa a gundumar Yushu ya kai 9138, an kaura da mutane 1962 da suka ji rauni zuwa sauran wurare domin samun jiyya, yanzu, mutane 8 sun warke.

Ya zuwa ran 18 ga wata da karfe 10 na safe, yawan mutanen da suka mutu a sakamakon girgizar kasa a gundumar Yushu ya kai 1706, kana mutane 256 sun bace, a yayin da mutane 12128 suka ji rauni, ciki har da mutane 1424 da suka ji rauni mai tsanani.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China