in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya kai rangadi zuwa gundumar Yushu da ke fama da girgizar kasa
2010-04-18 17:09:53 cri

A ran 18 ga wata da safe, shugaban kasar Sin, Hu Jintao ya isa gundumar Yushu da ke lardin Qinghai a arewa maso gabashin kasar, wadda a halin yanzu ke fama da girgizar kasa, domin yin jaje ga jama'ar da bala'in ya galabaitar da su tare kuma da ba da jagoranci kan ayyukan samar da agaji.


Da saukarsa a filin jirgin sama, sai nan da nan ya je wuraren da girgizar kasa ta yi musu muguwar barna. Sa'an nan, ya yi bincike a kan yadda ake samar da jiyya ga mutanen da suka ji raunuka da kuma yadda ake gudanar da rigakafin yaduwar cututtuka. Daga baya, Hu Jintao ya je wata makarantar marayu da ke gundumar Yushu, inda ya jajanta wa yaran da ke karatu a wurin.


Hu Jintao ya jaddada cewa, yanzu haka, aikin da ya kamata a sanya a gaban kome shi ne tsira da rayukan mutane, sa'an nan, a yi kokarin samar da jiyya ga mutanen da suka ji raunuka. Bayan haka, ya kamata a tsugunar da jama'a yadda ya kamata, kuma a tabbata an samar musu da abinci da ruwan sha mai tsabta da wurin zama da rigunan sanyawa. Har wa yau kuma, a gaggauta raya manyan ayyuka da farfado da karatu ga yara tun da wuri.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China