in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu aikin ceto suna kokarin taimakawa wadanda suke fama da bala'in girgizar kasa a gundumar Yushu
2010-04-17 17:33:55 cri
Ya zuwa karfe 8 saura minti 11 na ran 17 ga wata da safe, an riga an kwashe kwanaki 3 ana fama da bala'in girgizar kasa da ya auku a yankin Yushu na kabilar Tibet mai cin gashin kanta na lardin Qinghai da ke yammacin kasar Sin. Ko da yake sa'o'i 72, wato lokaci mafi muhimmanci wajen ceton mutane wadanda suke cikin buraguzan gine-gine sun riga sun wuce, amma bangarori daban daban suna ci gaba da yin namijin kokarinsu na yin aikin ceto tare da ba da jinya ga wadanda suka ji rauni da kuma yin jigilar masu raunuka sosai zuwa manyan asibitoci da kuma tsugunar da jama'a.

Jama'a masu sauraro, ya zuwa karfe 5 na ran 16 ga wata da yamma, yawan mutanen da suka rasu sakamakon wannan bala'in girgizar kasa ya riga ya kai 1144 tare da mutane 417 suka bace, mutane dubu 11 da 744 suka ji raunuka.

A ran 17 ga wata, a wani wurin yin aikin ceto da ke garin Jiegu na gundumar Yushu, inda aka gamu da bala'in girgizar kasa mai tsanani sosai, wakilinmu Ren Jie ya ga yadda ake aikin ceto, inda ya bayyana cewa, "Yanzu ina wani wurin yin aikin ceto da ke titin Shengli na garin Jiegu na gundumar Yushu. A bayyane gine-gine sun rusa gaba daya sakamakon wannan bala'in girgizar kasa. Kungiyar kasar Sin ta ba da aikin ceto ta kasa da kasa ta samu alama cewa, mai yiyuwa ne akwai mutane 3, wato maza 2 tare da mace daya da suke cikin wannan buraguzan gine-gine. Amma sabo da an rusa gine-gine sosai, an riga an tsara shirye-shirye yadda cetonsu ta hanya 2. Yanzu masu aikin ceto sun riga sun shiga buraguzan gine-gine domin kokarin ceton wadannan mutane 3."

Ya zuwa lokacin da wakilinmu ya aiko mana wannan bayani, rundunar 'yantar da jama'ar kasar Sin da rundunar 'yan sanda masu dauke da makamai sun riga sun aika da sojoji fiye da dubu 12 zuwa wuraren aikin ceto, kuma yawan mutanen da aka ceto ya kai 1253, kuma yawan masu rauni da aka ba su jinya ya kai 3831. Sannan hukumomin 'yan sanda masu kashe wuta sun aika da ma'aikatan kashe wuta fiye da dubu 1 domin yin aikin ceto.

Haka kuma, ana cikin gaggawa wajen ba da aikin jinya ga wadanda suka ji raunuka. Ya zuwa karfe 5 na ran 16 ga wata da yamma, rukunonin ba da aikin jinya 30 da ke kunshe da masu ba da aikin jinya 5880 sun riga sun isa yankunan da ke fama da bala'in girgizar kasa a gundumar Yushu. Bugu da kari, hukumomin zirga-zirga na motoci da na jiragen kasa da na jiragen sama na kasar Sin suna kuma kokarin ceton wadanda suka ji raunuka. Mr. Xia Xinghua, mataimakin direktan hukumar zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Sin ya ce, "Tun karfe 1 na ran 15 ga wata da rana, an soma isar da mutane wadanda suka ji raunuka sosai a filin saukar jiragen sama. Wasu daga cikin sun rasu lokacin da ake isar da su a filin jiragen sama. A irin wannan halin da ake ciki, mun tsai da kudurin cewa, dole ne a dauki matakin yin jigilarsu zuwa manyan asibitoci domin cetonsu cikin sauri."

A waje daya, ana tsugunar da jama'a kamar yadda ya kamata. Wakilinmu Ge Xiuyuan wanda ke neman labaru a gundumar Yushu ya aiko mana labari cewa, "Jiya, wato ran 16 ga wata, a filin sukuwar dawaki na gundumar Yushu, na ga yadda ake rarraba kayayyakin jin kai, kamar abinci da barguna da tantuna, har da murafu irin na zamani ga jama'a masu fama da bala'in girgizar kasa."

Ya zuwa yanzu, an riga an rarraba tantuna dubu 39 da barguna dubu 70 ko fiye da rigunan sanyi dubu 55 da abincin da yawansa ya kai ton 750 a yankunan da ke fama da bala'in girgizar kasa. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China