in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wen Jiabao ya kai ziyara garin Yushu domin jajantawa jama'ar da ke fama da bala'in girgizar kasa
2010-04-16 21:17:52 cri

Ran 16 ga wata, Mr. Wen Jiabao firaministan kasar Sin yana ci gaba da yin rangadi a garin Yushu na jihar Qinghai inda ake fama da bala'in girgizar kasa, ya ziyarci makaranta, da gidajen kula da marayu, da gidajen ibada, da filin da aka tsugunar da mutanen da suka rasa gidajensu domin jajantawa mutane na kabilu daban daban da ke fama da bala'in.

Mr. Wen Jiabao ya ce, dole ne mutane na kabilu daban daban su kula tare da taimakawa juna, da hada kansu domin fama da bala'i, wannan shi ne damar da muke da su wajen cin nasarar fama da bala'in.

Ya zuwa ran 16 ga wata da karfe 8 na safe, sakamakon bala'in girgizar kasar, an tabbatar da mutuwar mutane 791, kuma akwai mutane 294 da ba a gano su ba, mutane 11486 sun jikkata, kuma mutane 1176 daga cikinsu sunji rauni sosai. [Musa Guo]

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China