in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana kokarin ba da taimako ga yankin Yushu dake fama da bala'in girgizar kasa
2010-04-16 20:15:04 cri

Bayan abkuwar girgizar kasa a yankin Yushu, ma'aikatar harkokin zaman rayuwar jama'a ta kasar Sin da ta harkokin kiwon lafiya da ta zirga-zirgar jiragen kasa da ta kudi da kuma hukumar kula da harkokin hatsi ta kasar sun yi jigilar kayayyakin jin kai da masu ba da ceto zuwa yankin Yushu dake fama da bala'in girgizar kasa a lardin Qinghai cikin gaggawa.

A ran 16 ga wata, ma'aikatar harkokin zaman rayuwar jama'ar kasar Sin ta bayar da tantuna dubu 20 da rigunan sanyi dubu 50 da kuma barguna dubu 50 ga yankin Yushu.

A wannan rana, ma'aikatar harkokin kiwon lafiya ta kasar ta bayyana cewa, za a yi kokarin tattara kayayyakin kiwon lafiya daga wurare daban daban don ba da gudummawa ga yankin Yushu, da rage yawan mace-mace da raunin da mutane ke fama da shi, da kuma gudanar da aikin rigakafin yaduwar cututtuka a yankin. Ya zuwa ranar 16 ga wata da safe, ma'aikatar ta riga ta tura masu ba da jinya 1618 zuwa yankin.

Dadin dadewa, ma'aikatar zirga-zirgar jiragen kasa ta kasar ta bayyana cewa, ya zuwa 16 ga wata da karfe 2 da yamma, jiragen kasa 16 masu daukar kayayyakin jin kai da masu ba da ceto sun isa birnin Xi'ning, hedkwatar lardin Qinghai.

Ban da wannan, a ran 16 ga wata, ma'aikatar harkokin zaman rayuwar jama'a da ta kudi da hukumar kula da harkokin hatsi sun bayar da wata muhimmiyar sanarwa, inda aka tsai da kudurin ba da taimako na dan gajeren lokaci ga jama'a masu fama da bala'in a yankin Yushu don taimaka musu wajen warware matsalolin zaman rayuwarsu.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China