in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamata ya yi ma'aikatun da abin ya shafa su yi iyakacin kokari domin taimakawa jama'ar da girgizar kasa ta Yushu ta ritsa da su
2010-04-16 16:22:35 cri
A ranar 14 ga wata na safe, an yi girgizar kasa da karfinta ya kai digiri 7.1 bisa ma'aunin Richter a gundumar Yushu ta kabilar Tibet mai cin gabashin kanta da ke lardin Qinghai a yammacin kasar Sin. Ya zuwa ranar 15 ga wata da karfe 4 da rabi na yamma, jama'a da yawansu ya kai 791 sun rasu, tare da jikkatar wasu 11486, kuma gidajen jama'a kimanin 15000 sun rugurguje, kuma ana bukatar kauratar da jama'a kimanin dubu 100, don tsugunar da su a wasu wurare. Yanzu, kungiyar ceto ta riga ta garzaya zuwa yankunan da ke fama da bala'in girgizar kasa, an riga an ceci jama'a da yawansu ya kai sama da dubu daga baraguzan gidaje. Haka kuma, ma'aikatun da abin ya shafa za su ci gaba da tura kayayyaki ko kungiyoyin agaji zuwa yankunan da bala'in ya ritsa da su. Bayan abkuwan wannan girgizar kasa, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya jinkitar da ziyarar aikinsa a kasashen Venezuela da Chile, kuma zai dawo gida tun da wuri, kana, a ranar 16 ga wata na yamma, firaministan Sin Wen Jiabao ya isa wurin da bala'in ya shafa, bayan da ya sauka daga jirgin sama, ya je garin Jiegu da ke gundumar Yushu watau wurin da ke fama da bala'in sosai, ya je ganewa idonsa halin da aikin ceto ke ciki, kuma ya je gai da jama'a a asibitoci da makarantu. Ya ce,"Yanzu aikin da ke gaban kome shi ne a yi iyakacin kokari domin ceton mutane, bai kamata mu daina kokarinmu ba, musamman ma a cikin sa'o'i 72, dole ne mu yi iyakacin kokari."

A hedkwatar ba da umurni ga aikin yaki da girgizar kasa da ceton mutane da majalisar gudanarwa ta gina a tantuna, firaministan Wen ya bayyana cewa, kamata ya yi a tsugunar da jama'a yadda ya kamata, kuma ko ta kaka, ba za mu sa ko wane mutum da ya sha wahalar yunwa ko sanyi ba, ko kuma rashin ruwan sha mai tsabta ba, haka kuma kamata ya yi mu yi kokari domin farfado da wutan lantarki, don a ba da tabbaci ga amfanin ruwa, da samar da man diesel da injunan samar da wutan lantarki. Kazalika, Mr. Wen ya ba da umurni game da yaki da girgizar kasa ta biyo baya, da sake gine-gine da shimfida zaman doka da oda da gabatar da bayani game da girgizar kasa a bayyane.

Yanzu, ana gudanar da aikin yaki da girgizar kasa da ceton mutane kamar yadda ya kamata,an riga an farfado da harkokin sadarwa daga dukkan fannoni. A gun taron manema labaru da aka yi a ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa a ranar 15 ga wata na yamma, mataimakin direktan da ke kula da harkokin yaki da bala'i da ceton mutane na hukumar yaki da girgizar kasa ta kasar Sin Miao Chonggang ya ce, Bayan da aka yi girgizar kasa, an kaddamar da shirin ko-ta-kwana cikin hanzari a kasar, kuma mun tura kungiyoyi zuwa wuraren da girgizar kasa ta abku, kuma mun ba da umurnin aika da kungiyoyin ba da agaji cikin gaggawa domin yaki da bala'in girgizar kasa. A yankunan da girgizar kasa ta abku, kungiyoyin da ke kula da aikin ceto da sojojin 'yantar da jama'a da 'yan sanda masu kula da zaman lafiya da 'yan kwana-kwana, suna yin kokari tare, kuma, ana gudanar da aikin yaki da girgizar kasa da aikin ceto cikin armashi.

Haka kuma shugaban sashen kula da harkokin ceton mutane na ma'aikatar kula da harkokin jin dadin jama'a ta kasar Sin, Zhouming ya bayyana cewa, bayan da aka farfado da hanyoyi da zirga-zirgar jiragen kasa da jiragen sama, matsalar karancin kayayyaki da ke damuwar yankunan da bala'in ya shafa za ta samu kyautatuwa cikin kwanaki 2 masu zuwa. Ya ce, Yanzu, babbar matsala ita ce, karancin tantuna da barguna da tufafi masu maganin sanyi, da abinci. Za a iya tsugunar da mutane kimanin dubu 100 a cikin tantunan da aka shirya da yawansu ya kai 38800, a ganina, wannan ya isa.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China