in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wen Jiabao ya isa yankin Yu Shu domin ba da jagoranci ga ayyukan ceto
2010-04-16 09:19:41 cri

A ranar 15 ga wata da yamma, memban zaunannen ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar kwaminis ta Sin kana firaministan kasar Sin Mr Wen Jiabao ya isa yankin Yu Shu domin jajantawa jama'ar wurin da ba da jagoranci ga ayyukan ceto. Ya nuna cewa, babban aiki a yanzu shi ne ceton mutane.

A wannan rana da dare, bayan da ya mika gaisuwa ga jama'ar da suke fama da bala'i da masu gudanar da aikin ceto, Wen Jiabao ya kira taro a wurin domin sauraron yadda ake gudanar da ayyukan ceto da ba da umurni a fannin aiki. Wen Jiabao ya ce, manyan ayyuka guda 10 na yanzu su ne, da farko, ceton jama'a; sai kula da ayyukan jiyya; kokarin sake tsugunar da jama'ar wurin; sake farfado da gine-ginen more rayuwa; shirya tinkarar yiwuwar abkuwar kananan girgizar kasa; ba da kudin tallafi; gudanar da ayyukan kimantawa yadda ya kamata da tsai da tsarin sake bunkasa wurin cikin hanzari; tabbatar da oda ta zamantakewar al'umma; ba da labari a fili; sannan da kara ba da jagoranci.(Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China