Jaridar Aminiya ta ce, an zabi shugaban Bingu Wa Mutharika na Malawi a matsayin sabon shugaban kungiyar tarayyar Afirka wato AU, bayan da wa'adin shugabancin Mu'ammar Ghaddafi na Libya ya cika, kuma bai samu komawa karo na biyu ba. Don haka ma ya ce, ''Dan uwana shugaban Malawai zai karbi ragamar shugabanci daga gare ni,' in ji Ghaddafi a yayin bude taron kwanaki uku da aka shirya a Addis Ababa.
Shugaba Ghaddafi ya tafiyar da shugabancin tarayyar ne wajen cimma burinsa na kafa 'dunkulalliyar tarayyar Afirka', al'amarin da bai samu cikakkiyar nasara ba a tsawon watanni 12 da ya yi yana rike da ragamar mulki. Amma duk da haka ya ce, zai ci gaba da wannan burinsa, don ganin ya hada kan nahiyar Afirka. Ghaddafi ya kara da cewa, 'Ba sai ina rike da wani mukami ba, zan ci gaba da zama a gaba-gaba wajen hada kan Afirka.'
Kungiyar tarayyar Afirka na shirin amincewa da bukatar da shugaban Senegal ya gabatar kan yadda za a taimaki wadanda suka rasa gidajensu a sanadiyyar girgizar kasa da aka yi a Haiti, musamman ma a duba yiwuwar 'kafa musu wata kasa a Afirka.' Shugaba Abdoulaye Wade ya ce, tarihi ya tabbatar da cewa, asalin mutanen Haiti sun fito ne daga bayi 'yan Afirka. Tuni shugaban kwamitin tarayyar Jean Ping ya sanar da shugabannin Afirka a wajen taron cewa, za a duba wannan bukata. Haka kuma tarayyar Afirka ta bude asusun agaza wa mutanen Haiti a Bankin raya ci gaban Afirka wato AFDB.
Jama'a masu karatu, bayan haka kuma bari mu sake duba wani labari da muka samu daga jaridar Aminiya ta kasar Nijeriya, wadda aka fita a wannan mako, inda aka bayyana cewa, Buhari ya fice daga jam'iyyar ANPP ta kasar.
Jaridar Aminiya ta ce, 'dan takara na shugaban kasa a karkashin jam'iyyar ANPP a zaben shekara ta 2003 da 2007, Janar Muhammadu Buhari ya fice daga jam'iyyar ANPP.
Wata takarda da Janar Buhari ya aike wa jam'iyyar a ran 1 ga watan Fabarairu ce ta tabbatar da ficewar Janar Buhari daga jam'iyyar.
Takardar ta bayyana cewa, janar din ya shiga jam'iyyar APP ce, wadda daga baya ta koma ANPP a ran 15 ga watan Afrilu na shekarar 2002, sabo da lura da barazanar daga jam'iyyar PDP mai mulkin kasar nan, don haka ne ya zabi jam'iyyar da yake ganin za ta ba shi damar da zai bayar da tasa gudumowa wajen bunkasawa da tabbatar da dimokuradiyya a Nijeriya.
Janar din ya ce, 'a shekara ta 2003 da 2007 na samu damar zama 'dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar. Na gode kuma zan ci gaba da godiya ga jam'iyyar kan amincewar da ta nuna mana na zama wakilinta a wadannan lokuta biyu. Kuma abubuwan da suka faru a wadannan zabubbuka sanannu ne ga al'ummar kasar nan da kasashen duniya. Sai dai tun shekara ta 2007, wasu alamu suka fara bayyana sabanin da zai yi wuya a sami fahimtar juna tsakanina da shugabannin jam'iyyar, a sakamakon haka, aka jingine mai yawan 'ya'yan jam'iyyar a gefe kan al'amuran gudanar da ita. Wannan ya kawo mana cikas wajen bayar da duk wata gudumowar a-so-a-gani ga kasarmu a karkashin wannan jam'iyya.'
Janar Buhari ya ce, sakamakon haka ne, ya dauki wannan shawara maras dadi ta ficewa daga Jam'iyyar All Nigerian Peoples Party wato ANPP, daga ranar Litini 1 ga watan Fabrairu na shekarar 2010.(Danladi)