in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yau ya rage sauran kwanaki 30 a kaddamar da bikin baje koli na duniya a birnin Shanghai
2010-04-01 19:24:28 cri

Yau ya rage sauran kwanaki 30 a kaddamar da bikin baje koli na duniya a birnin Shanghai. A karo na farko bikin baje koli na duniya da ke da tsawon tarihi na shekaru 159 zai samu dama bayyana a wata kasa mai tasowa. Domin shirya wani kyakkyawan biki cikin nasara da ba za a iya mantawa ba, jami'ai masu shirya bikin da ma'aikata kana da mazauna birnin Shanghai masu kirki suna gudanar da ayyukan share fage cikin tsanaki. Bikin baje koli na duniya na Shanghai yana zuwa.

A ran 1 ga wata, ma'aikata masu kula da ayyukan bikin baje koli na duniya sun yi rantsuwa a filin da ke gaban babban dakin nune-nune na kasar Sin da ke cikin harabar bikin baje koli na duniya, inda suka yi alkawarin cewa, za su yi namijin kokari wajen gudanar da ayyukan share fage domin ba da hidima sosai ga baki daga wurare daban daban.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China