in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jia Qinglin ya halarci dandalin tattaunawa na hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki da ke tsakanin kasashen Sin da Afrika ta kudu
2010-04-01 18:20:38 cri

A ran 31 ga watan Maris, a Pretoria, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Jia Qinglin ya halarci dandalin tattaunawa na hadin gwiwa na tattalin arziki da ciniki da ke tsakanin kasashen Sin da Afirka ta kudu, a gun dandalin ya yi wani jawabi mai suna "zurfafa hadin gwiwa don tabbatar da moriyar juna".

Jia Qinglin ya bayyana cewa, kasar Sin tana son ci gaba da kara amincewa juna a fannin siyasa tare da Afirka ta kudu, da kara yin hadin gwiwa na tattalin arziki da ciniki bisa manyan tsare-tsare. Ta haka, Jia Qinglin ya gabatar da shawarwari 4 da ke dangane da kara yin ciniki da kara zuba jari da kara karfin gwamnati a fannin ba da hidima da kara yin hadin gwiwa da ke tsakanin kamfanonin kasashen biyu.

Jia Qinglin ya kara da cewa, kasar Sin tana son yin kokari tare da kasashen Afirka da ke hade da Afirka ta kudu wajen ba da gudumawa a fannonin sa kaimi ga yin hadin gwiwa na tattalin arziki na duniya domin farfado da shi da kuma tabbatar da zaman lafiya a duniya cikin dogon lokaci da neman jituwa a cikin zaman al'umma.

Ministan cinikayya da masana'antu na kasar Afrika ta kudu Rob Davies da ya halarci dandalin ya nuna babban yabo ga muhimmiyar rawa da kasar Sin ta taka a fannin warware rikicin kudi na duniya da sa kaimi ga farfado da tattalin arzikin duniya da bunkasuwar kasashen duniya, kuma ya bayyana cewa, yin hadin gwiwar tattalin arziki shi ne wani mihimmin aiki na dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da ke tsakanin kasashen biyu, kuma wannan aiki yana taka muhimmiyar rawa wajen bunkasuwar tattalin arzikin Afirka ta kudu.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China