in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jia Qinglin ya halarci dandalin tattaunawa na hadin gwiwa na tattalin arziki da ciniki dake tsakanin kasashen Sin da Afrika ta kudu
2010-04-01 15:36:06 cri

A ran 31 ga watan Maris, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Jia Qinglin ya halarci dandalin tattaunawa na hadin gwiwa na tattalin arziki dake tsakanin kasashen Sin da Afrika ta kudu, inda ya ce, ya kamata a ci gaba da zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannin tattalin arziki da ciniki domin kawo moriyar juna.

Shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Jia Qinglin wanda ke yin ziyara a kasar ya halarci taron, kuma ya yi jawabi kan zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki da kawo moriyar juna. Jia Qinglin ya kuma yaba wa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Sin da Afrika ta kudu a fannin tattalin arziki da ciniki sosai, ya ce, "A shekarun baya, bisa goyon bayan da gwamnatocin kasashen biyu suka nuna da kokarin da 'yan kasuwa na kasashen biyu suka yi, hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki da kasashen biyu suka yi ta samu bunkasuwa da habakawa sosai, kana ta kara yin hadin gwiwa ta hanyoyi dabam daban, kuma ta samu sakamako mai kyau. Sabo da haka, hadin gwiwarsu ta taka muhimmiyar rawa kan hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China