Jia Qinglin ya gabatar da kyawawan fata gare su, ya ce, na farko ta fanning yin kokari wajen samun bunkasuwa a kasuwannin kasashen Afrika. Sai, yin hobbasa don taimakawa kasashen Afrika wajen kyautata zaman rayuwar al'umma a wurin, domin kiyaye kwarjinin masana'antunsu da na kasar Sin. Kana da batun kafa tsarin hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da cinikayya da kasashen Afrika, domin daidaita lamura tare.
Wakilan masana'antun da ke halartar taron, sun bayyana cewa, masana'antun Sin a kasar Afrika ta kudu za su ci gaba da kiyaye manufar samun moriyar juna cikin jituwa tare, da yin kokari wajen raya sana'o'insu da gudanar da hakikanin ayyuka a wurin, domin kokarin fadada hadin gwiwa kan sha'anin tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, da kara yin kokari wajen sa kaimi ga sha'anin raya tattalin arzikin kasar Sin da sada zumunci tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika.(Bako)