in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gama gina yankin yin bikin baje koli na duniya na Shanghai
2010-03-31 16:58:54 cri

A ran 1 ga watan Mayu, za a bude bikin baje koli na duniya na Shanghai. A yayin bikin, yawan kasashen da za su shiga bikin zai fi yawa a tarihin bikin baje koli na duniya. A ran 30 ga wata, a birnin Shanghai, Yang Xiong, mataimakin shugaban birnin Shanghai kuma mataimakin darektan kwamitin kula da harkokin bikin baje koli na duniya na Shanghai ya gaya wa 'yan jarida fiye da dari daya na gida da waje. Ana iya cewa, a halin yanzu dai, ana kusan gama gina yankin yin bikin baje koli na duniya, kuma ana yin aikin shirya abubuwan nune-nune yadda ya kamata. Birnin Shanghai zai yi iyakacin kokarinsa na tabbatar da lafiya da odar bikin baje koli na duniya, ta yadda masu yawon shakatawa za su yi ziyara da kyau.

Bikin baje koli na duniya da za a yi a Shanghai ya kai matsayi na farko a tarihin bikin baje koli na duniya daga fannoni da yawa. Wannan biki shi ne karo na farko da za a yi bikin baje koli na duniya a kasar mai tasowa, kuma yawan kasashe da kungiyoyin da za su shiga bikin ya kai 242, kana shi ne karo na farko da za a yi bikin a tsakiyar yankin birnin mai girma, kuma za a mai da hankali kan bunkasuwar birane.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China