in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jia Qinglin ya gana da shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma
2010-03-31 09:09:08 cri

A ran 30 ga wata, a Pretoria, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Jia Qinglin ya gana da shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma.

Jia Qinglin ya bayyana cewa, kasashen Sin da Afirka ta kudu duk su kasashe masu tasowa ne, bangarorin biyu suna fuskantar batun bunkasuwar tattalin arzikinsu da kyautata zaman rayuwar jama'a, kuma suna da moriya daya a kan harkokin kasashen duniya. Kasar Sin tana mai da hankali a kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, kuma tana son ci gaba da kara yin hadin gwiwa tare da kasar Afirka ta kudu, da maida hankali kan bunkasuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da ke tsakanin kasashen biyu.

Jacob Zuma ya bayyana cewa, ziyarar da Jia Qinglin ya yi tana da muhimmiyar ma'ana ga kara bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Ban da haka kuma, Jacob Zuma ya nuna babban yabo ga ra'ayoyi da matakan da kasar Sin ta dauka wajen warware batun sauyawar yanayi, kuma ya bayyana cewa, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga samun sakamako mai kyau a gun taron Copenhagen, yana fatan kasashe masu tasowa da ke hade da kasar Sin da kasar Afirka ta kudu za su kara yin mu'amala, don sa kaimi ga aka samun sakamakon da ke dacewa da moriyar kasashe masu tasowa a gun taron Mexico, da kiyaye moriyar kasashe masu tasowa.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China